Rayuwar aure ba fim ba ce, ba kuma zaman shaukin soyayya kawai ba ne.
Lokacin neman aure soyayya na iya sa mutum ya ga komai da kyau, amma bayan aure, rayuwa ta hakika ce ke farawa, mutum biyu ne suka hadu, kowannensu da halayyarsa, tunaninsa da tarbiyya da yadda kuma yake kallon rayuwa.
Saboda haka, aure ba ya dorewa da kalaman soyayya kadai, yana bukatar gaskiya, amana, hakuri, fahimtar juna da girmama juna.
Akwai lokacin da za ku yi sabani, amma abin da ke ceto aure shi ne ku iya tsayar da gaskiya, ku fadi gaskiya cikin ladabi, ku saurari juna, sannan ku yarda a gyara kuskure sannan a yafewa juna.
Ma'auratan da suka fahimci cewa ba lallai ne su yi daidai a komai ba, amma dole su mutunta juna, su ne suka fi samun zaman lafiya da dorewar aure.
Allah Ya sanya soyayya, rahama da fahimtar juna a tsakanin ma'aurata Ameen